ƙwayoyin cuta Coronaviruses na daga cikin wani babban rukunin da aka sani suke jawo cuta daga mura da aka fi sani zuwa cututtuka mafi tsanani kamar su cutar numfashi na gefen larabawa wato Middle East Respiratory Syndrome (MERS) da cutar hanyoyin numfashi mai tsanani wato Severe Acute Respiratory Syndrome (SARS).
An gano sabuwar cutar COVID-19 a shekarar 2019 a garin Wuhan na ƙasar China. Wannan sabuwar cutar coronabirus ce baʻa taɓa samun irinta a mutum ba.
Wannan kwas ya bada gabatarwa zuwa cutar COVID-19 da sauran cututtukan hanyoyin numfashi da ke tasowa kuma an haɗa shi don ma'aikatan kiwon lafiya, masu gudanar da rahoton cututtuka da masu aiki a majalisar ɗinkin duniya, ƙungiyoyi na duniya da masu zaman kansu NGOs.
Tunda an kafa sunan bayan an kirkiro abun, duk lokaci da aka ce nCoV yana nufin COVID-19, cutar da kwayar cutar coroabirus da aka gano ke jawo shi.
Lura cewa abubuwan da ke cikin wannan kwas a halin yanzu ana sabunta su don nuna jagorar kwanan nan. Kuna iya samun sabbin bayanai kan wasu batutuwa masu alaƙa da COVID-19 a cikin darussa masu zuwa:
Alurar riga kafi: Tashar rigakafin COVID-19
Matakan IPC: IPC don COVID-19
Gwajin saurin gano cutar Antigen: 1) SARS-CoV-2 antigen fast diagnostic gwajin; 2) Mahimmin la'akari don aiwatar da SARS-CoV-2 antigen RDT